
Rundunar ƴan sanda a jihar Legas ta fara gudanar da bincike kan mutuwar wani karamin yaro bayan da aka yi masa allura a wani asibiti da ke unguwar Ogombo a Legas.
Jami’in hulda da jama’a na ƴan sanda a Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa, NAN, lamarin a jiya Alhamis.
Hundeyin, mai muƙamin Sufeto na ƴan sanda, ya ce ƴan sandan sun samu labarin lamarin, amma babu wanda ya bayar da rahoto a hukumance game da lamarin.
“Eh, muna sane da abin da ya faru. Mahaifin marigayin ya zo ofishin mu amma ya ki rubuta ƙorafi.
“Su ma ma’aikatan asibitin sun zo ofishin na mu ba tare da yin wani bayani ba. Don amfanin kowa, an tura su zuwa CID na jihar don gudanar da cikakken bincike,” inji shi.
NAN ya rawaito cewa an nuna wani mutum yana kuka a faifan bidiyo da ya yadu, inda ya koka kan yadda wani ma’aikacin jinya ya yi wa ɗansa allurai hudu, wanda ba a ambaci sunansa ba kuma ya mutu sakamakon alluran da aka yi masa.
Mutumin ya yi ikirarin cewa an yi wa dan wasu allurai ne a ranar Laraba kuma ya rika yin amai bayan kowace allura.
Ya jaddada cewa likitan ya yi wa yaron allurai hudu ba tare da yaron ya ci abinci ba kuma da ga ƙarshe ya mutu.
NAN ya kara da cewa faifan bidiyon ya kuma nuna gawar yaron a kan gado tare da mahaifin na kuka a gefensa.