Home Kanun Labarai Saraki zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben Atiku 2019

Saraki zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben Atiku 2019

0
Saraki zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben Atiku 2019

Shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki shi ne mutumin da aka zaba wanda zai jagoranci kwamatin yakin neman zaben Atiku Abubakar Domin zama Shugaban Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben 2019.

Kakakin uwar jam’iyyar PDP na kasa ne ya bayyana sunayen ‘Yan kwamatin a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter.

Sanarwar ta bayyana cewar Bukola Saraki ne Shugaban kwamatin yakin neman zaben yayin da Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya zama Shugaban kwamatin shiyyar Arewa maso yamma.

Haka kuma an zabi Gwamnan Gombe Ibrahim Dankwambo a matsayin Shugaba na shi yyar Arewa maso gabas, yayin da Gwamnan Binuwai Samuel Otorm ya zama Shugaban kwamatin shi yyar Arewa ya tsakiya.

Gwamnan jihar Ekiti mai barin gado Ayo Fayose shi je Shugaban kwamatin na shi yyar kudu maso yamma yayin da Gwamna David Umahi ya zama Shugaban kwamatin shiyyar kudu maso gabas, Gwamnan jihar Ribas Wike shi ne zai jagoranci kwamatin a shiyyar kudu maso kudu.

Haka kuma, an zabi Kabiru Tanimu Turaki SAN a matsayin Shugaban kwamatin sashin Shariah na kwamatin yakin neman zaben a cewar sanarwar.