
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya kalubalanci yadda dukan matan aure ke karuwa a Arewacin Najeriya. Sarkin ya nuna rashin jin dadinsa akan yadda ake cin zarafin mata babu kakkautawa.
Sarkin ya bayyana hakan ne a taron kungiyar mata Musulmi ta FOMWAN, taron da kungiyar ta shirya a birnin Kano. Sarkin ya nuna rashin gamsuwarsa, akan yadda wasu ke fakewa da addini suna dukan matansu.
“A makon da ya gabata, muka samu labarin wani magidanci ya kashe matarsa sabida mugun duka da yayi mata,” Aacewar Sarkin Kano.
Sarki Sunusi ya bukaci a hada hannu da karfe da kungiyoyi masu zaman kansu da ba na gwamnati ba, domin kawo karshen irin cin zarafin da ake yiwa mata a cikin gidajensu, akan abinda bai kai ya kawo ba.
A lokacin da yake nasa jawabin, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu wakilcin kwamishiniyar mata ta jihar Kano, Hajiyar Yardada Maikano, ta bayyana cewar, dole bangarorin gwamnati guda uku su himmatu wajen samarwa mata da matasa abin dogaro da kai ta fannin Noma.
Gwamnan ya bayyana cewar, matasa su ne kashin bayan cigaban wannan al’ummar, barin su kara zube ba zai taba samarwa da al’ummar kasarnan da mai ido ba.