Home Ilimi Ƴar shekara 10 ta lashe gasar karanta haruffan kalmomi a Borno

Ƴar shekara 10 ta lashe gasar karanta haruffan kalmomi a Borno

0
Ƴar shekara 10 ta lashe gasar karanta haruffan kalmomi a Borno

Wata yarinya ƴar shekara 10, mai suna Aisha Modu Mustapha daga makarantar firamare ta Sanda Kyarimi ta lashe gasar karanta haruffan kalmomi da ka, na shekara-shekara ta Inara a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Aisha ta karanto haruffan kalmomi kamar su ‘Whirligig, Quarreling, Administration, Willingly, Spaceless, Peasant da sauransu, inda ta doke abokan karawar ta, Muhammad Muhammad Dawule, daga Makarantar Firamare ta Gamborou da Bukar Muhammad daga makarantar Ibrahim Damchida.

Gidauniyar ta ba wa wadanda suka yi nasara a gasar ta kimiyya da karanta haruffan kalmomi kyautar na’ura mai ƙwaƙwalwa ta tafi-da-gidanka, kudade da kuma kayan karatu na dubban daruruwan nairori.

Da ta ke jawabi bayan kammala gasar a ranar Alhamis, wacce ta kirkiro da gasar, Aisha Waziri Umar, ta ce an shirya gasar ne domin tallafa wa da cigaban ilimi a jihar Borno.

Ta kara da cewa alfanon da a ke samu ya wuce batun iya turanci domin yana taimaka wa yara wajen samun kwarin-gwiwa yin magana a bainar jama’a da kuma fahimtar karatu, gami da samun hikimar bada amsa a takure.