Home Siyasa Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Adamawa ya fice daga PDP zuwa NNPP

Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Adamawa ya fice daga PDP zuwa NNPP

0
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Adamawa ya fice daga PDP zuwa NNPP

 

 

Hammatukur Yattasuri, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Jihar Adamawa ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar NNPP.

Da ya ke jawabi a wani biki a Yola a yau Talata, Yattasuri ya bayyana cewa ya koma jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ne domin zai fi yi wa jama’arsa hidima.

Ya kuma yi alkawarin cewa al’ummar mazaɓarsa za su ƙara sharɓar romon dimokaraɗiyya idan aka sake zaɓen shi a matsayin dan majalisar wakilai a karkashin sabuwar jam’iyyar ta sa.

Shima da yake nasa jawabin, Hamman Ribadu, sakataren NNPP na arewa maso gabas ya bayyana ficewar ɗan majalisar a matsayin wani babban kamu ga jam’iyyar.

Ya ce Yattasuri ya koma jam’iyyar a daidai lokacin da ya dace, yana mai ba shi tabbacin goyon bayan da ya dace.

Shi kuma Saidu Salmana, Shugaban NNPP na Ƙaramar Hukumar Jada, ya bayyana Yattasuri a matsayin mutum mai gaskiya wanda yake da kyawawan halaye da kuma yawan mabiya.

Ya yaba masa da shiga jam’iyyar, inda ya ce ya dauki matakin da ya dace.