
Daga Abba Wada Gwale
Sojojin Najeriya sun fatattaki ‘yan ta’addan Boko Haram a yayin da su ka kaiwa sojojin hari a wani sansaninsu da ke shiyyar garin Yamteke da ke ƙaramar hukumar Gwoza.
A sanarwar da kakakin sojin ƙasarnan Birgediya-Janar Sani Usman Kukasheka ya bayar, ya ce arangamar ta faru ne a ranar Talatan nan da misalign karfe 8:35.
Ya ce sojojin sun nunawa yan ta’addar ƙarfin wuta da dabarun yaƙi a yayin da maharan ke yunƙurin afka musu da motoci maƙare da bam da kuma ’yan ƙunar baƙin wake.
Daga nan ne sai sojojin suka yi musu ruwan harsashi, suka kashe shabiyar kuma su ka ƙwato motar yaƙi ƙirar Panhard Vehicule Blinde Leger.

Ya ƙara da cewa sojojin sun ƙwato alburusai da dama da mota ƙirar Hilux wacce aka dasa bindigar harbo jirgi a bodinta.
Sai dai an rasa soja guda a yayin arangamar.