Home Kanun Labarai Tambuwal ya gargadi ‘yan Shia kan yin zanga zanga a Sokoto

Tambuwal ya gargadi ‘yan Shia kan yin zanga zanga a Sokoto

0
Tambuwal ya gargadi ‘yan Shia kan yin zanga zanga a Sokoto
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

Gwamnatin jihar Sokoto a ranar laraba tayi gargadi ga ‘yan Shiah a jihar akan cewar ba zata lamunci duk wata zanga zanga a jiyar da sunan juyayi a Sokoto.

Kwamishinan Shariah na jihar kuma antoni janar, Sulaiman Usman, shi ya bayar da wannan gargadi a madadin gwamnatin jihar Sokoto a lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan wani zama na musamman kan batun tsaro a jihar.

Kwamishinan yace, wasu bayanan sirri da gwamnati da jami’an tsaro suka samu ya nuna ‘yan Shiah a jihar na nan na shirin yin wata zanga zanga da sunan wani juyayi wadda zata iya kawo yamutsi a jihar.

“Akwai bayanai da suke nuna wasu aikace aikacen ‘yan Shiah a jihar ba abinda zasu kawo sai zaman dar-dar da rikici.”

“A saboda haka, idan ba a yi hattara ba, zaman lafiyar da ake amfana da shi a jihar, na iya samun tasgaro idan aka zubawa ‘yan Shiah ido zasu lalata shirin zaman lafiya a jihar” a cewar antoni janar kuma kwamishinan Shariah a jihar ta Sokoto.

Ya kara da cewa, “muna masu haramta dukkan wani shiri na yin zanga zanga a ko ina a fadin jihar Sokoto, don haka duk wanda ya karya wannan doka kada ya zargi kowa ya zagi kansa”

A dan haka ana gargadin ‘yan Shiah da su kiyaye dokokin da hukumomin gwamnati suka gindaya domin samun dorewar zaman lafiya a jihar.

A dan haka, ina amfani da wannan dama a madadin gwamnatin Sokoto nayi kira ga al’umma da musamman ‘yan Shia su kiyaye bin doka da oda. A cewar Sulaiman Usman.

A nasa jawabin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Mohammed Abdulkadir yace a shirye hukumomin tsaro suke a dukkan fadin jihar domin ganin an kiyaye dokokin da gwamnatin jihar ta gindaya.

A sabida haka, kwamishinan ‘yan sanda na kira ga ‘yan Shia su kasance masu bin doka da oda don kaucewa fishin jami’an tsaro a jihar. A cewarsa, jami’ansa a shirye suke don bada kariya ga zaman lafiyar jihar.

Kamfanin dillancin labaru na kasa NAN ya ruwaito cewar an zauna domin tattaunawa a jihar, wanda bangarorin jami’an tsaro suka halarta da syka hada da ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya na SSS da NSCDC da kuma jami’an hukumar gidan yarin jihar.