
Shugaban gidauniyar Tompolo, Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da “Tompolo” ya bayar da tallafin kayan abinci na Naira miliyan 150 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihohin Delta, Bayelsa da Rivers.
An mika kayayyakin ne a hukumance ga wakilan wadanda abin ya shafa a fadin jihohin uku a jiya Litinin a Warri, Delta.
Da yake gabatar da kayayyakin, a madadin gidauniyar, babban sakatarenta, Dokta Paul Bebenimibo, ya ce kayayyakin sun hada da: buhunan shinkafa 2400, buhunan wake 100 da kuma buhunan gari 200.
Sauran sune: doya guda 5000 ; kilo 200 na dabino; Katan 600 na man gyaɗa da kwali 2000 na taliyar Indomie.
Bebenimibo ya ce tallafin zai rage raɗaɗin ambaliyar ga wadanda abin ya rutsa da su, sannan kuma zai taimaka musu wajen koma wa gidajensu da gaggawa yayin da su ke jiran gudumawa daga sauran bangarori.
Ya ce an kafa gidauniyar domin taimaka wa masu karamin ƙarfi a yankin.