
Kungiyar Brighton da ke buga gasar firimiyar inga ta sanar da cewa Enock Mwepu ya yi ritayar dole yana da shekara 24 sakamakon gano ciwon zuciya da ake kyautata zaton na gado ne.
Dan wasan tsakiyar ya rataye takalmnnsa ya kwanta rashin lafiya ne a lokacin hutun kwallon kafar ƙasashe, inda gwaje-gwaje da akai masa ya nuna cewa yana fama da ciwon zuciya ne.
Dan wasan tsakiyar, ɗan ƙasar Zambia, ya koma Ingila ne daga kungiyar kwallon kafa ta Red Bull Salzburg a lokacin kakar 2021 kuma ya buga wasanni 27 a Brighton, inda ya ci kwallaye uku.
A yanzu dai ta faru ta kare, inda rashin lafiya ta tilasta masa rataya bayan da Mwepu ɗin ya kamu da rashin lafiya a lokacin da ya ke cikin jirgi a kan hanyarsa ta saduwa da ƴan wasan Zambia a lokacin hutun ƙwallon kafar ƙasashe na wasan cikin gida, lamarin da ya sa ya shafe lokaci a asibiti kafin ya koma Brighton domin a gwada lafiyar zuciyarsa.
Shugaban Brighton, wacce ake wa kirari da Seagulls, Tony Bloom ya gaya wa shafin yanar gizon kungiyar din: “Dukkan mu mun ji takaicin a kan Enock. Shi da iyalinsa sun yi makonni masu ban tausayi kuma yayin da muke godiya kawai da ya zo a wannan lokacin, ya ga irin wannan aiki mai ban sha’awa da aka yi a irin wannan shekarun. A matsayinmu na kungiya za mu ba shi dukkan kulawa, taimako da goyon bayan da za mu iya don samun cikakkiyar lafiya, sannan kuma yayin da ya yanke shawara kan matakai na gaba a rayuwarsa. ”
Kocin Brighton Roberto De Zerbi ya kara da cewa: “Na yi hakuri da Enock. Kafin in iso sai na kalli dukkan ‘yan wasan, kuma shi dan wasa ne ina matukar sha’awar aiki da shi. Za mu yi duk abin da za mu iya don taimaka masa.”
Gwaje-gwaje sun nuna cewa Mwepu na fama da matsalar zuciya ta gado wanda ke bayyana kansa daga baya a rayuwa kuma ba koyaushe ake iya gane shi ba a jiki.