Home Labarai Wasu mutum biyu sun shiga hannu sakamakon sayar da tabar wiwi a gidan kurkuku

Wasu mutum biyu sun shiga hannu sakamakon sayar da tabar wiwi a gidan kurkuku

0
Wasu mutum biyu sun shiga hannu sakamakon sayar da tabar wiwi a gidan kurkuku

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta gabatar da wasu mutumbiyu a babbar kotu a Legas sakamakon danke su da aka yi suna kasuwancin wiwi a gidan kurkuku na Kirikiri dake Legas.

Bayo Abdulrahman dan shekaru 33 da shadiat Obafemi ‘yar shekaru 26, sun shiga hannu sakamakon kamasu da tabar wiwi da ta kai nauyin giram 100 a cikin kurkukun da yafi kowanne tsaro a Najeriya.

Tuni dai mutanen biyu suka amsa laifinsu, bayan da suka amsa laifi ne, me gabatar da kara Jeremiah Aernan ya shaidawa kotun laifin da mutanan suka aikata a rubuce. kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.