Home Labarai Yadda Maryam ta sokawa mijinta wuka har ya mutu yayin da yake sallah

Yadda Maryam ta sokawa mijinta wuka har ya mutu yayin da yake sallah

0
Yadda Maryam ta sokawa mijinta wuka har ya mutu yayin da yake sallah

Makusancin dangin marigayi Bilyaminu Bello, wanda matarsa ta kashe shi ta hanyar sassoka masa wuka har ya mutu, dan uwan tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa  Bello Halliru Mohammed, ya shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN yadda Mayam ta kashe mijinta da kanta.

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Maryam a kufule take, ta zo iya wuya, a ranar Asabar da daddare, bayan da ta yi ido biyu da sakwannin karta kwana a wayar mijinta, wadan da suke dauke da kalaman soyayya, abinda yake tabbatar mata da cewar, yana soyayya da wata daban.

Amma wani makusanci ga danginsu, wanda yayi bayanin cikin halin alhini, ya Bayyanawa DAILY NIGERIAN cewar, sun yi zaton sabanin da aka samu tsakanin ma’auratan biyu ya wuce, lokacin da Kawun Maryam ya shiga cikin al’amarin domin sasantawa.

Kamar yadda ya shaida mana, Maryam ta samo sharbebiyar wuka a dakin girki, sannan ta jira lokacin da mijinta ya kabbara Sallar Isha, sannan ta kaddamar masa da mummunan hari, inda ta sassoka masa.

“A lokacin da ta soke shi a bayansa da kirjinsa da kuma ‘ya ‘yan marenansa, nan take ya fadi kasa yana marari tare dafatan ta taimake shi. Maryam na kallonsa, kwance male-male cikin jini, yana rokonta da ta taimaka masa don ceton rayuwarsa.

“An jiyo shi yana cewar ‘Maryam ki taimake ni… Maryam ki taimake ni, har ya kai gargarar mutuwa yana kiran da ta agaje shi, amma shiru tayi tsaye tana kallonsa, har ya kasa yin wani katabus, sannan ta bara.

“Maryam kawai cewa take, Allah ne ya toona maka asiri, tana maimaitawa, har yace mata ga garinku nan, ya cika a wajen.

“Awa daya bayan wannan dambarwa ta auku, lokacin da taga baya ko motsi, sannan ta nemi taimakon makota da su taimaka mata sanya shi a cikin mota domin ta kaishi asibiti.

“Asibitin farko da suka je, sun ki yadda su duba shi sabida halin da suka ganshi suka ce sai da dan sanda, sai da suka je wani asibitin ne,sannan jami’an asibitin suka kirawo ‘yan sanda, kuma Maryam ta tabbatar da cewar ita ce ta cakawa mijin nata wuka har ya mutu” A cewar dangin mamacin.