
Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Hukumar kula da qwallon qafa ta qasar ingila, FA ta bayyana cewa ta amince da tayin da qasa Nijeriya tayi mata na buga wani wasan sada zumunci domin tunkarar wasan cin kofin duniya.
Tawagar qwallon qafar ta Ingila za ta buga wasan sada zumunta da ta Nigeria a shirin da take yi na fafatawa a gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha.
Ingila na fatan yin wasa da Super Eagles ta Najeriya ne a filin wasa na Wembley dake birnin Landan a ranar 2 ga watan Yuni na wannan shekarar da ake ciki
Haka kuma tawagar ta Ingila za ta yi wasan sada zumunta da tawagar yan wasan qasar Costa Rica a Elland Road ranar 7 ga watan Yuni, sannan ta wuce zuwa qasar Rasha domin fara wasanni.
Ingila wadda mai koyarwa Gareth Southgate ke horar wa tana rukuni na bakwai da ya qunshi qasashen Tunisia da Panama da kuma qasar Belgium.
Nigeria kuwa tana rukuni na hudu da ke dauke da qasashen Argentina da Iceland da kuma Croatia.
Mai koyar dayan wasan Najeriya, Gernot Rohr, ya bayyana cewa wasa da qasar ingila zai taimakawa yan wasansa da gofewa da kuma sannan yadda zasu tunkari manyan qasashe a qasar Rasha.
Acikin wannan satin ne dai Najeriya ta buga wasannin sada zumunta guda biyu da qasashen Poland da Serbia inda tasamu nasara akan Poland xin daci 1-0 yayibda kuma tayi rashin nasara akan Serbia daci 2-0.
Itama ingila ta buga wasannin sada zumunta guda biyu da qasashen Holland da Italiya inda tasamu nasara akan qasar Holland daci 1-0 sannan kuma tayi kunnen doki 1-1 da qasar Italiya.