Home Labarai Za a mayar da asibitin fadar shugaban ƙasa na kuɗi

Za a mayar da asibitin fadar shugaban ƙasa na kuɗi

0
Za a mayar da asibitin fadar shugaban ƙasa na kuɗi

Sakamakon wasu matsaloli da suka dabaibaye babban asibitin dake fadar shugaban ƙasa, gwamnati ta ƙuduri aniyar mayar da shi na kuɗi, a cewar babban sakataren fadar shugaban ƙasa, Alhaji Jalal Arabi.

Alhaji Arabi dai ya fitar da wannan jawabi ne ta hannun maimagana da yawun ofishinsa Mista Attah Esse ya rabata ga manema labarai.

Alhaji Arabi, yayi ƙarin bayani kan dalilin da ya sanya aka ƙuduri aniyar mayar da asibitin na kuɗi, ya ƙara da cewar, sakamakon rashin kuɗaɗen gudanar da asibitin da kuma irin ɗawainiyoyin da yake yi, ga kuma daɗa tsuke bakin aljihu da gwamnati take yi, ya sanya suka ƙuduri aniyar mayar da shi na kuɗi.

Yace, yin hakan kaɗai zai bayarda damar yin sauye-sauye da zasu sake fasalta asibitin domin ya dace da zamani. Domin kuwa a cewarsa, asibitin na fadar Shugaban ƙasa, mutane na zuwa ne a duba lafiyarsu a basu magani ba tare da an caje su ko kwabo ba.

Ya kara da cewa gwamnati ba zata iya jure kashe kuɗi haka ba.

Yaya kuke kallon wannan ƙuduri, shin ko ya dace a mayar da asibitin fadar shugaban kasa na kuɗi?