
Wata kotu a ƙasar Sifaniya ta bayar da umarnin tsare ɗan wasan Brazil Dani Alves a gidan yari har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci a kan shari’ar da ake yi masa kan zargin cin zarafin wata mata.
A ranar Juma’a ne aka tsare ɗan wasan mai shekara 39 a birnin Barcelona.
Alves wanda tsohon ɗan wasan Barcelona ne ya musanta zargin cewa ya ci zarafin wata mata a wani gidan rawa.
Kan wannan batun dai tuni ƙungiyar da ɗan wasan ke taka wa leda Pumas UNAM ta ƙasar Mexico, ta ce ta soke kwantiragin ɗan wasan nan take.