
‘Yan ta’addar da yawnsu ya kai mutum dari 200 sun dirarwa karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, inda suka kashe mutum 10 tare da yin garkuwa da mata da yawa, da kuma kunnawa gidaje wuta da jikkata mutane da yawa.

Wasu da abin ya far a kan idonsu, un bayyana cewa, maharan sun zo ne akan babura da kuma mota kirar akori kura guda biyu samfurin Hilux.