
Fatan alhairi tare da adduar samun nasara ga gwamnatin ka, domin samun nasarar wannan gwamnati zai kara wanzar da cigaba mai dorewa ga rayuwar miliyoyin talakawan wannan Jihar.
‘
Maigirma Gwamna, hakika, muna kara yabawa da kokarin da kakeyi wajen samar da cigaba a wannan Jiha ta mu. Sai dai, bisa dukkan alamu kanayin tuyar ka amma kana mantawa da albasa. Ma’ana yankunan karkara, wanda shi ne mafi rinjaye a Jigawa baya samun kulawar da ya dace da shi.
‘
Ranka yadade, ko ka taba zagayawa yankunan karka? Ina nufin ziyar bazata, ba ziyarar biki ba wanda ‘yansiyasar kauyukan mu ke daukar hayar matasa domin su fito bakin hanya suna maka tafi da san barka, kai kuma kana murmushi kana murna cikin zuciyar ka gamsu cewa lallai mutane suna jin dadin mulkin ka. Ina rokon ka, ka shiga kauyuka kaga yanda tarun samari, masu lafiya da karfin jiki suke yini a kasan bishiya domin babu aikin yi.
‘
A yayin da kake karanta wannan wasika, wasu da ga cikin mu sun tafi ci-rani kudancin Najeriya, wasu kuma suna shirin tafiya. Sani kanka ne Yallabai, wannan tafiya tana kunshe da sharruka da hatsaruka daban-daban. Wasu da ga ciki suna koyo muna nan dabi’u su shigo mana da su jiha, wasu kuma suna kamuwa da cutukan zamani irin ‘cuta mai karya garkuwa jiki’ (HIV/AIDS). Su dawo su ci gaba da yada wannan cuta tsakankanin al’umma.
‘
Idan ka kayi ziyara gidan fursun, za ka tarar mafiya yawancin daurarru daga kauyuka su ke, kuma laifin sata ne. Ranka yadade, mutanen karka suna son dandana dadin rayuwa amma talauci yayi musu katutu ga kuma jahilci.
‘
Ranka ya dade, ko kasan akwai dubban mutane a rugagen fulani da suke rayuwa amma ba’a taba koyar da su ibada ba? Ko ka san akwai milliyoyon mutanen kauyuka da basu taba rike allo ba ko alkalami? Ko ka san akwai dattijan da suka rayu shekaru sama da 70 amma basu iya tsarki ba ballantana azo zancen ibada? Basa samun kulawa saboda kawai su mutan karkara ne, Ranka ya dade, kasani Allah zai tamabayeka akan amanar addinin sa, wanne gudun muwa kabayar wajen tsare shari’a, wajen yada addinin sa?
‘
Ranka yadade, kataimaki kanka ta hanyar duba yanda zaka kai ilimi musamman na addini ga lungu da sako na karkara a Jigawa. Domin amana ce Allah yabaka, kuma hakika Allah zai tambayeka.
‘
Ranka ya dade, ina baka shawara, ka duba yiyuwar samar da manomacin rani a yankunan karkara yanda matasan mu zasu shagaltu da ayyukan raya kasar su. Wannan abu ne mai sauki matukar ka kudiri niyyar aikatawa domin taimakon Allah yana jiranka matukar ka himmatu.
‘
Ranka ya dade, kayi hakuri da kalamai na, hankalina ne a tashe. Idan baka dauki matakin da ya dace ba, ina za mu sa kan mu nan da shekaru masu zuwa? Ya kake ganin za mu rayu? A yanzu ma matsalolin fiyade da sace-sace sun yawaita kuma duk sanadiyar nuna halin ko-inkula da shugabanni sukeyi ne.
‘
Daga karshe, ina fata za ka duba wannan koken namu da kyakykyawar zuciya tare da niyyar aikata abun da ya da ce.
Wa Salam, Ka huta lafiya.
‘
Muhammad Buhari Muhammad
Birnin kudu, Jihar Jigawa, Najeriya.
0803 412 0635.
Advocate for Social Justice
Abubakar Abdullahi, Dip. Crime Magt, Adv.Law, B. Sc., CAC, LTC,
Dutse,
Jigawa State, Nigeria.
css120009@gmail.com
08028485429
Abubakar Abdullahi, Dip. Crime Magt, Adv.Law, B. Sc., CAC, LTC,
Dutse,
Jigawa State, Nigeria.
css120009@gmail.com
08028485429