
Hukumar Hisba ta Jihar Kano, reshen Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ta kai wani sumame babbar Makarantar Sakandare ta Grammar da ke garin Dawakin inda ta kama wasu ɗalibai da askin banza a kansu, wai domin murnar kammala karatun sakandire.
Dakarun Hisbah ɗin sun yi nasarar damƙe da dama daga cikin ɗaliban, waɗanda su ka yi askin da a ke wa laƙabi da “ba kwaɓa”.
Bayan dakarun sun kama da na kama wa, wasu kuma sun tsere, sai su ka zaunar da su a harabar makarantar, inda su ka aske musu gashin tas.
Wannan na ƙunshe ne a wata gajeriyar sanarwa da jami’in Sashen Fasahar Sadarwa ta Zamani na Hisbah din, Abdulwahab Said Ahmad, a shelkwatar ta da ke birnin Kano.
Wasu daga cikin daliban dake kammala Jarrabawar gama Sikandiren sune sukai gyaran gashi da aski daya saba da al’adar Hausawa da kuma Tarbiyya.