Home Labarai Tsohon kwamishinan Kwankwaso ya zama shugaban PDP na Kano

Tsohon kwamishinan Kwankwaso ya zama shugaban PDP na Kano

0
Tsohon kwamishinan Kwankwaso ya zama shugaban PDP na Kano

Jam’iyyar PDP ta zabi Alhaji Ado Kibiya a matsayin sabon shugaban ta na jihar Kano.

Jam’iyyar ta sanar da sabon shugaban ne a safiyar yau Lahadi.

Kibiya, wanda ya taba zama Kwamishinan noma a lokacin Gwamnatin Rabi’u Musa Kwankwaso daga 1999 zuwa 2023, ya shiga zaben da goyan bayan mafiya yawan jagororin jam’iyyar.

Kibiya ya samu nasara kan ƴan takara biyu da suka shiga zaben kuma tuni dai aka rantsar da sabon shugaban na PDP a filin wasa na Kano Pillars da ke Sabongari